Daga Aliyu Abdullahi Fagge
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Usaini Muhammad Gumel , ya bayyana cewa ya gamsu da yadda ake gudanar da ƙarashen zaɓen da bai kammala a jahar.
Kwamishinan ƴan sandan ya ziyarci, Remin keɓe, Zango , Kwachiri, Rijiyar Lemo, Alasawa , Fagge Dandali, waɗanda suke a ƙananan hukumomin Fagge da kuma Unggo.
Tunda safiyar ranar Asabar Ma’aikatan hukumar zaɓe suka kai kayan aikin zaɓen a rumfunan da za a yi zaɓen , na ƴan majalissar tarayya 2 da kuna na ƴan majalissun jaha 13.
CP Usaini Gumel ya ce, abun ya bashi sha’awa domin mutanen jahar Kano sun yi ƙoƙari sun fito da yawansu dan kaɗa ƙuri’unsu maza da mata.
“kuma sun ƙara burgeni wajen yin haƙurin bin layi .
Ƙarashen zaɓe: Rundunar yan sanda a kano ta Sanya dokar taƙaita zirga-zirga al’umma
Kwamishinan ya ƙara da cewa a wasu tashoshin zaɓen da aka bi , sun tarar da ko’ina, mutane na ta ƙoƙarin ganin kowa ya kaɗa ƙuri’arsa ba tare da tsangwama ba.
Dalibai matan da aka sace na Jami’ar Tarayya ta Gusau sun shagi Iskar ‘yanci
“kuma wani abu da ya ƙara burge mu shi ne , su matasa a mafi yawancin guraren da muka ziyarta suna yi mana alƙawarin cewa yawancin masu kawo matsala a zaɓen daga wasu guraren matasa ne suke tahowa daga wata unguwa suyi abinda suke so su fita.
Dan hakane ma matasan yankunan da ake yin zaɓen suka haɗa kai da ma’aikatan tsaro , a tabbatar da duk wanda yazo dan tayar da hankulan su za a yi masa abinda ya dace.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa sauran guraren da ake yin zaɓen sun samu labarrin komai yana tafiya daidai.
Rahotanni sun bayyana cewa an fasa akwatina guda 2 masu namba 029 da kuma 023 a Rijiyar Lemo dake ƙaramar hukumar Fagge.
Kazalika an fasa wani akwatin a Zango dake ƙaramar hukumar Ungoggo , wanda tuni rahotanni suka bayyana cewa an cafke wasu daga ciki.