Daga Abdulrashid B Imam
Rundunar Yansanda ta kasa reshen jihar kano ta sanya dokar takaita zirga zirgar al’umma a dukkanin fadin jihar, daga ƙarfe 12 na dare zuwa ƙarfe 5 na yammacin gobe Asabar, Sakamakon Zaben cike gurbi da za’a gudanar a wasu kananan hukumomin jihar.
” Kwamishinan yan sanda na Kano CP Usaini Gumel yace a fadawa jama’a cewa an Sanya dokar taƙaita zirga-zirga, Kuma Rundunar baza lamunci karya dokar ba, don tabbatar da ganin an gudanar da zaben lami lafiya”.
A karo na biyu: Abba Gida-gida ya baiwa shugabannin kananan hukumomin Kano shawara
Kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren juma’ar nan .
Yace Rundunar ta shirya tsaf domin dakile duk wasu aiyukan bata gari a wuraren da za’a gudanar da zaben, sannan ba’a yarda wani wanda ba ya cikin masu yin zabe ya je Inda za’a kada kuri’a ba.
” An ɗauki wannan matakin ne don hana tada hatsaniya a yayin zaɓen, Kuma duk wanda muka kama da makami ko Kuma mutum ya fita ya je Inda za’a yi zabe to zai daidana kudar sa”. Inji SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito za’a gudanar da ƙarshen zaben ne a wasu wuraren kada kuri’a kimanin 200 a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar kano, wadanda suka hadar da zaɓe yan majalisun tarayya da na majalisar dokakin jihar.