Direban jirgin sama ya yi artabu da maciji a kan kujerar zamansa a sararin samaniya

Date:

Daga Abdullahi Danbala Gwarzo

 

An yaba wa wani matuƙin jirgin ɗan Afirka ta Kudu kan nasarar saukar gaggawa da ya yi, bayan da ya lura da wani maciji nau’in gamsheƙa a ƙarƙashin kujerar zamansa.

 

Rudolph Erasmus ya ɗauko fasinjoji huɗu daga birnin Cape Town zuwa arewacin Nelspruit da safiyar ranar Litinin amma saboda artabun da ya yi da gamsheƙar ya sa shi saukar gaggawa, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

 

Mun yi takaicin yadda muka rasa kujerar gwamnan kano – APC

Direban ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Time Live cewa “ina duba ƙarƙashin kujerata, kawai sai na ga macijin na ƙoƙarin mayar da kansa ƙarƙashin kujerar”.

 

Sarkin Kano ya Jagoranci Sallar Jana’izar Matar Gwamnan Kano na farko

Sarar gamsheka zai iya kashe mutum cikin mintuna 30 idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

 

Minista harkokin sufurin jiragen sama ta Afirka ta kudu ya yaba da jarumtar Mr Eramus, kamar yadda shafin yanar gizo na news24 ya ruwaito.

 

Direban jirgin yace ya shiga yanayi mai rikitarwa wajen fada wa fasinjojin ainihin abin da ya sa ya yi saukar gaggawar.

 

“Na fada musu cewa akwai matsala., akwai maciji a cikin jirgin. Ina da yaƙinin cewa yana ƙarƙashin kujera ta don haka za mu yi saukar gaggawa”.

 

Ya yi ƙoƙarin ganin ya yi saukar gaggawa a birnin Welkom dake Afirka da Kudu.

 

Injiniyoyin da suka caje jirgin ba su ga gamsheƙar ba, inji Mr Eramus.

 

Ya ce yana sa ran komawa bakin aikinsa a ranar Laraba.

 

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...

Tinubu ya yi wa Buhari abun da Buharin ya kasa yi wa kakana- Jikan Shagari

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Nura Muhammad Mahe, jikan tsohon shugaban...

Yanzu-yanzu: Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fice daga...

Gwamnatin Jihar Kano ta fara bincike kan mutuwar wasu ɗaliban makarantar Sakandare biyu

  Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Makoda, ya...