Akwai gwamnoni da Ministocin za mu tuhuma bayan May 29

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ce ta kammala shirye-shiryen kama wasu gwamnonin da wa’adin mulkinsu ke karewa wadanda ake zargi da ayyukan rashawa, da kuma wasu gurbatattun masu rike da mukaman gwamnati bayan miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

 

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, shi ya bayyana haka ranar Alhamis yayin tattaunawa da Jaridar Daily Trust.

 

Sai dai Bawa bai bayyana sunaye ko kuma yawan waɗanda suke shirin kamawa ba da zarar sun suka daga kan mulki.

 

A Najeriya dai, gwamnoni na cikin jami’an gwamnati da ke da kariya wadda ya hana a a kama su idan suna kan mulki.

 

Shugaban na EFCC ya ce akwai ma’aikatun gwmanati guda biyu da hukumar ke bincike a kansu a halin yanzu saboda ayyuka da suka saɓa wa ka’ida da suke yi.

 

A cewarsa, a ɗaya daga cikin ma’aikatun an yi almundahanar kuɗaɗe ta N4bn na wasu kwangiloli kusan 20 da.

 

Bawa ya ce, “A yanzu haka, muna binciken ma’aikatu biyu da aka biya kuɗaɗen har sau biyu a cikinsu.

 

“Waɗannan kwangiloli ne da aka yi tun shekarar 2018, sannan wasu mutane masu karfin hali suka fito da suka bayyana batun.

 

Ya ce an buga takardun bogi a cikin ma’aikatun, sannan da haɗin-bakin wasu ma’aikata, aka kirkiri takardun karya tare da biyan kuɗi.

 

Bawa ya ce muddin aka mayar da harkoin gwamnati ta hanyar zamani, ba za a samu irin waɗannan badaƙaloli ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...