Ramadan: Abba Gida-gida ya bukaci wadanda sukai takara da su zo su haɗa kai don ciyar da kano gaba

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya yi wa daukacin al’ummar Musulmi barka da shigowa watan azumin Ramadan, inda ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa Jihar kano addu’ar samun zaman lafiya.

 

Domin samun zaman lafiya da yafiya a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, zababben Gwamnan yana gayyatar al’ummar Kano ciki har da ‘yan takarar da ya kayar a zaben 2023, da su hada kai da shi wajen ganin sun kai jihar kano ga nasara da ake fata.

 

Sarkin Kano ya taya Abba Gida-gida Murnar lashe zaben gwamnan jihar

Ya ce watan Ramadan yana ba da damar yin sulhu da yafiya musamman a tsakanin ‘yan siyasa domin samar da zaman lafiya da ci gaban jihar baki daya.

 

A cikin wata sanarwa da kakakin zababben gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu kuma ya aikowa kadaura24, ya ce ba mu da wani gari da yafi Kano, don haka ya zama wajibi ‘yan jihar su bada gudunmawarsu don inganta zaman lafiya da gina tattalin arziki, zamantakewa da Al’adun jihar kasancewar kano ita ce cibiyar kasuwancin Najeriya.

 

Ya kuma shawarci ’yan kasuwar dake sayar da kayan abinci a fadin kasuwannin Kano da su guji cin mummunar riba tare da tausaya wa masu karamin karfi don samun damar yin bude baki cikin sauƙi, yana mai tabbatar wa al’umma cewa gwamnati mai jiran gado za ta himmatu wajen kawar da fatara ta hanyar karfafawa matasa, tallafawa masu karamin karfi da kuma kyautata jin dadin jama’ar Jihar.

 

Ya kuma bukaci Limamai da Malamai a dukkan masallatai da ke fadin kananan hukumomin jihar 44 da su yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba a Kano yayin da sabuwar gwamnati ta ke shirin amsar mulkin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...