Daga Maryam Abubakar Tukur
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi kira da a gaggauta sauya kwamishinan zabe na jihar Kano Amb Abdu Zango daga jihar.
Bayan wata zanga-zangar lumana da aka gudanar a ofishin INEC a ranar Laraba shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya gabatar da bukatar a gaggauta sauya Amb Abdu Zango daga jihar Kano.
Jam’iyyar mai mulki ta kuma yi kira da a gudanar da bincike kan al’amuran da suka biyo bayan ayyana Abba Kabir Yusuf na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
A ranar Litinin din da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Abba Kabir Yusuf na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano, inda ya bayyana sakamakon zaben a Kano, jami’in tattara sakamakon zaɓen na jihar, Farfesa Doko Ibrahim, mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya ce Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’u 1,019,602 wanda ya samu nasara, akan abokin takarar sa Nasir Gawuna na jam’iyyar APC wanda ya zo na biyu da kuri’u 892,705.
Abbas, wanda ya samu wakilcin mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Barr. Abdul Adamu Fagge, ya dage da cewa ya kamata a bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
“muna zargin kwamishinan Zaɓen da haɗa baki da yan jam’iyyar NNPP a kano, tun a zaben farko da akai Kuma mun gabatar da korafi akan hakan Amma ba a ɗauki mataki ba, ga shi kuma ya kara tabbatar da zargin da muke yi masa Inda ya tsallake dokar zabe kuma ya bayyana sakamakon zaben, bayan kamata yayi ya ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, don haka muka kira da tsancha shi”. Inji Abdullahi Abbas
A cewarsa, adadin kuri’u 273,442, aka kada wanda kuma aka ce an soke su, kuma kuri’un sun ninka adadin dake tsakanin NNPP da APC wanda ya kai 128,897.
Ya ci gaba da cewa, hakan ya ci karo da tanadin sashe na 24, 51 na dokar zabe ta shekarar 2022, sashe na 62 na dokokin INEC da ka’idojin gudanar da zabe a shekarar 2022, da kuma na 4.2.16, bayanin kula na 32 a shafi na 84 da abu 6 na tebur a shafi na 93 na Littafin Jagoran Zabe, 2022.
A nasa jawabin jami’in hukumar zabe wanda ya karɓi masu zanga-zangar Lawan Sani Kofar Sauri yace sun karɓi koken da yan jam’iyyar APC sukai Kuma zasu ɗauki matakan da suka dace akan korafe-korafen.