Daga Kamal Yahaya Zakaria
Tsohon dan takarar shugaban kasa a tutar jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya gana da kwamitin Zaman lafiya na jihar kano, sakamakon katowar zaɓen gwamnan wanda za’a gudanar a ranar asabar 18 ga watan maris na 2023.
Kadaura24 ta rawaito kwamitin dai ya kudiri aniyar ganawa da duk jagororin jam’iyyun Siyasa na Kano da Sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin zabe don ganin an gudanar da zaben gwamna lafiya a jihar kano.
A wata sanarwa da Kwankwaso yasa a sashihin shafin aa na Facebook ya ce ya yi farin cikin karbar bakuncin mambobin kwamitin zaman lafiya na jihar Kano.
” Na sake jaddada kudurinmu na ganin mun bada hadin kai don ganin an gudanar da zabe na gaskiya da adalci”. Inji Sanata Kwankwaso
“Ina kuma yabawa kwamitin bisa kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya a jiharmu mai albarka”. A cewar jagoran NNPP
Kwamitin dai wanda yake karkashin dan Amar din Kano Alhaji Aliyu Harami Umar da AB Mahmoud SAN sun ce sun ziyarci Kwankwason ne domin neman hadin kan sa da na yan jam’iyyar NNPP don ganin an gudanar da zabe mai zuwa lafiya ba tare da an sami hatsaniya ba.
Ko a safiyar ranar alhamis din nan sai da kwamitin suka gana da gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, Inda shi ma suka tunasar da shi nauyin da ke wuyan sa na ganin ya bada duk gudunmawar da ya dace don gudanar da zabe lafiya.