Daga Abdulrashid B Imam
Sufeto-Janar na ƴansanda, IGP Usman Alkali ya fasa kawo Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaro na gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, zuwa jihar domin gudanar da zabe.
Yanzu haka dai IGP din ya mayar da CP Faleye Olaleye daga jihar Ebonyi zuwa Kano domin ya jagoranci rundunar a lokacin zabe.
IGP din ya kuma sake tura karin wasu manyan jami’ai zuwa jihar domin karfafa tsaro a lokacin zabe.
Kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta gani na baya-bayan nan, IGP din ya tura AIG Sani Dalijan domin ya jagoranci shiyya ta daya a Kano.
Haka kuma takardar ta nuna cewa Ita Lazarus Uko-Udom ne zai jagoranci Kano ta tsakiya, inda DCP Umar Iya zai kasance na biyu a matsayin shugaba.
Alkali ya kuma aike da DCP Abdulkadir El-Jamel domin kula da kananan hukumomin Albasu, Gaya, Rogo, Takai, Ajingi, Garko, Wudil da Sumaila.
A kananan hukumomin Rano, Bebeji, Bunkure, Doguwa, Kiru, Kibiya Tudunwada dake jihar Kano ta kudu kuwa, IGP ya tura DCP Adamu Ngojin domin ya kula da tsaron a can haka.
IGP din ya kuma tura DCP Abaniwonda Olufemi zuwa Kano ta Arewa, tare da ACP Adamu Sambo a matsayin babban kwamandan sa na biyu.
Kamar yadda sabuwar takardar ta nuna, DCP Auwal Musa ne zai jagoranci CID, yayin da DCP Aminu Maiwada zai dauki nauyin gudanar da ayyuka a hukumar ta Kano a lokacin zabe.