Mun sha alwashin magance matsalolin da aka samu da BVAS a zaɓen gwamnoni – INEC

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Shugaban hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa da ‘yan ƙasar cewa za a yi amfani da na’urar BVAS a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da ke tafe a makon gobe.

Farfesa Yakubu ya tabbatar da haka ranar Asabar a lokacin ganawa da kwamishinonin hukumar zaɓe na jihohi a shalkwatar hukumar da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Ya ce za a yi amfani da na’urar BVAS a zaɓen, domin kuwa a cewarsa ana sake duba na’urorin domin kauce wa matsalolin da suka bayar a wasu wuraren a zaɓen makon da ya gabata.
“A ranar zaɓe za a yi amfani da na’urar BVAS domin tantance masu kaɗa ƙuri’a da tattara sakamakon zaɓe,” in ji Yakubu
“Aiki da na’urar ta BVAS ya taimaka wajen tsabtace aikin tantance masu zaɓe kamar yadda muka gani a zaɓukan da suka gabata”.
”Tun makon da ya gabata, hukumar zaɓe ta ƙara ƙaimi wajen sake duba na’u’rorin domin kauce wa matsalolin da aka samu a wasu wuraren a zaɓen da ya gabata, musamman kan ɗora sakamakon zaɓe a rumbun adana sakamakon da muka tanadar a shafin intanet. Kuma muna da tabbacin cewa na’urorin za su yi aiki kamar yadda ya kamata.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...