Daga Halima Musa Sabaru
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce ‘yan takarar da aka zaba a majalisar dattawa da ta wakilai a zaben na ranar Asabar da ta gabata za su karbi takardar shaidar cin zabe a mako mai zuwa.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya sanar da hakan a ranar Asabar a wani taro da suka yi da kwamishinonin zabe, a Abuja.
A cewar Yakubu, za a baiwa zababbun Sanatoci satifiket din su ne a ranar 7 ga Maris, yayin da takwarorinsu na Majalisar Wakilai za su karbi nasu a ranar 8 ga Maris.
Shugaban na INEC ya kuma bayyana cewa an bayyana sunayen wadanda suka yi nasara a kan kujeru 423 na ‘yan majalisa, inda ya kara da cewa an bayyana karin zaben a mazabu 46.
An bayyana cewa, kujeru 98 daga cikin kujeru 109 na majalisar dattawa da kuma kujeru 325 daga cikin kujeru 360 na majalisar wakilai an bayyana wadanda suka lashe zabukan su.