Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gamayyar kungiyoyin farar hula na jihohin Arewa, sun bukaci shugaban kasa Muhammad Buhari da ya yi watsi da kiraye-kirayen da wasu suke yi, na ya kori shugaban EFCC da wasu masu zanga-zanga da aka biya suke yi.
Kungiyoyin farar hular (CSO) sun kada kuri’ar amincewa da shugabancin Abdulrasheed Bawa na hukumar EFCC tare da bayyana shirye-shiryen ci gaba da marawa hukumar baya ne domin sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.

Kungiyar a wani taron manema labarai da ta gudanar a Kano a ranar Alhamis din da ta gabata, kuma shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na Kano Ambasada Ibrahim A. Waiya, yace suna zargin wani gwamna ne ke daukar nauyin masu zanga-zangar, wanda shi kansa da makusantansa ana zargin su da uwa na cin hanci da rashawa.

“Mu ‘ya’yan kungiyoyi masu zaman kansu na Jihohin Arewa, muna fatan kara karfafa wa shugabannin EFCC kwarin gwiwar ci gaba da gudanar da aikin sa na yaki da cin hanci da rashawa ba tare da la’akari da kabila, addini ko yanki ba don kawar da cin hanci daga kasarmu Nigeria,” in ji Waiya.
“Muna so mu yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da ya yi watsi da kiraye-kirayen a korar shugaban EFCC da masu zanga-zangar ke yi wanda kuma wani gwamna ne ya ke daukar nauyinsu wanda shi da makusantansa ake zargin su da cin hanci da rashawa.
“Muna so mu bayyana karara cewa a matsayinmu na mambobin Gamayyar kungiyoyin farar hula na jihohin Arewa, daga jihohin Arewa goma sha tara da kuma babban birnin tarayya Abuja, mun amince da shugabancin da Abdulrasheed yake yiwa EFCC, kuma za mu ci gaba da marawa Hukumar bayan don ganin ya sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa.’