Wata Kungiyar Siyasa ta baiwa daliban Tudun Wada da Doguwa su 35 tallafin JAMB kyauta

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo
wata kungiyar Siyasa mai suna  Alh. Yahya support Organisation for Dan Ado 2023 ta gudanar da rabon fom din jarrabar neman gurbin karatu a manyan makarantu wato JAMB ga wasu dalibai su kimanin 35 a yankin kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada.
Da yake mika fama-faman ga dalibai Alhaji yahaya Muhammad wanda shi ne darakta janar na kungiya yace sun baiwa daliban tallafin ne sakamakon matsananci hali da al’umma suka sami kansu ciki a asanadiyyar Chanjin kudi.
Talla
Yace kungiyar su tana da bukatar ganin matasa sun yi karatu domin sai da Ilimi dan Adam yaje sanin waye shi Kuma Mai ya kamata ya yi, don inganta Rayuwar da ta al’ummar sa.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
” A wannan karon dalibai 35 ne daga kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa suka ci gajiyar tallafin saboda mawuyacin halin da ake fuskanta Wanda babban bankin Nigeria ya sanya mutane a cikin, hakan tasa muka ga dacewar bada wannan tallafi a irin wannan lokaci”.
Daga karshe ya yi kira da sauran kungiyoyi da gwamnati da kuma dukkan wanda Allah ya ba su iko dasu cigaba da tallafawa mussamman a harkar ilimi duba da yanayin da ake ciki a wannan lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...