‘Yan siyasa da masu zabe su ne barazana ga zaben 2023 – Attahiru Jega

Date:

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce ‘yan siyasa da ma masu zabe su ne babbar barazana ga nasarar zabukan da ke tafe na kasar, na ranar 25 ga watan nan na Fabrairu da kuma na 11 ga watan Maris.

Ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatar da babban jawabi jiya Talata a Abuja, a wurin taron wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman tare da hakuri da juna da kuma yin zabe cikin kwanciyar hankali da ba tare da wata matsala ba, wanda cibiyar Da’awa da Tabbatar da Jin Dadin Jama’a ta babban masallacin tarayya da ke Abuja ta shirya.

Talla

Farfesan ya ce wadanda ke kiran kansu ‘yan siyasa, da suka hada da masu takara su ne rukunin masu ruwa da tsaki a harkar da kusan za a iya cewa ba a ga wani sauyi na kirki a kan yadda suke gudanar da al’amuransu da suka danganci zabe ba tun 1999.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

”Burinsu kawai shi ne su yi nasara ta ko wane hali, inda suke daukar zabe a matsayin wani abu na ko a mutu ko a yi rai. Kamar yadda suke yi tun 1999, suna ci gaba da yin haka, kuma za su iya yin hakan a 2023,” in ji shi.

Jega ya kara da cewa; ”Yadda ba a hukunta su kan abin da suke yi, haka kuma suke kara dilmiya cikin magudi da miyagun abubun da suke yi. Wanda wannan ka iya zama babban kalubale ga zabukan 2023.’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...