Karancin kudi: Ganduje zai gayyaci manajojin Bankunan dake kano

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur
 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kalubalanci manufar sauya fasalin kuɗi kasar nan da gwamnam babban bankin Nigeria (CBN) Godwin Emefiele ya yi da cewa an yi hakan ne da gangan, Saboda bai Sami tikitin tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC ba.
Ganduje ya yi kalubalen ne a yayin gangamin yakin neman zabe, wanda aka gudanar a Tsanyawa, Lahadi, inda ya gabatar da ‘yan takarar gwamna da mataimakan gwamna, tare da dan takarar sanata da sauran ‘yan takara.
A cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya aikowa kadaura24, yace Gwamnan ya jaddada cewa, “Gwamnan CBN yana yin haka ne kawai domin ya haifar da rudanin babu gaira ba dalili a zabe mai zuwa.
Talla
 Bai fito da wannan tsarin da kyakyawar niya  ba, kawai yayi hakan ne saboda ya kasa samun tikitin takarar shugaban kasa a tutar babbar jam’iyyar mu ta APC.” inji Ganduje
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
 Sanarwar ta ƙara da cewa daya daga cikin matakan da gwamnan ya dauka domin ragewa al’ummar kano wahalhalun da chanjin kuɗin ya haifa shi ne , “Za mu gayyaci manajojin Bankuna nan ba da jimawa ba domin jin ta bakin su kan matsalar da ta haifar da karancin sabbin takardun kudin a bankuna.
” Su zo su bayyana mana dalilin da ya sa har yanzu al’ummarmu ke shan wahala a kan wannan batu na chanjin kudi. Kuma zan ziyarci bankunan daya bayan daya don in ganewa idanun na halin da al’umma suke cikin da Kuma yadda za’a magance matsalolin.” Ganduje ya jaddada
 Ganduje yace akwai tsari da gwamnatin sa take shirin yi na bada tallafi ga al’ummar dake kananan hukumomi 44, domin rage musu wahalhalun da Gwamnan CBN ya jefa su a ciki .
 A fadar Hakiman Kananan Hukumomin Kunchi da Tsanyawa, Gwamnan ya bukaci shugabannin al’umma da su kara wayar da kan jama’ar yankin cewa,. Wahalhalun da suke fuskanta, Gwamnan CBN ne da kansa ya ke haddasasu, da gangan don ya kawo tsaiko jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...