Ku saki sabbin kuɗi ko na kwace lasisin filayen ku – Zulum ya gargadi bankuna

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi bankunan kasuwanci a jihar cewa gwamnatinsa za ta ƙwace lasisin filin duk bankin da ya gaza saka sabbin takardun naira a na’urorin cire kuɗi na ATM.

 

Gwamnan ya yi gargaɗin ne ranar Juma’a a birnin Maiduguri lokacin da ya kai ziyara don gane wa idonsa irin dogwayen layuka da wahalar da jama’a ke fuskanta na ƙarancin sabbin takardun kuɗin.

Talla

“Duk bankin da ba shi da niyyar cika ATM ɗinsa da sababbin takardun kuɗi don sauƙaƙa wa al’umma wahalhalu, za mu ƙwace filin gininsa nan take,” in ji gwamnan cikin wata sanarwa da kakakinsa Isa Gusau ya fitar.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Sanarwar ta ce ran Gwamna Zulum ya ɓaci ne lokacin da ya tarar da wani dogon layin cirar kuɗi, inda ATM ɗaya ne kacal yake aiki cikin 10 da ke wurin.

 

“Kamar yadda kuke gani, talakawa ne kawai a kan layi…An ce wasu tun ƙarfe 3:00 na dare suke a nan, wasu ma ba su ci komai ba. Sababbin kuɗin da tsofaffin duka babu, wanda hakan ke shafar harkokin kasuwanci tare da ƙuntata wa mutane,” a cewar Zulum.

 

Gwamnan ya ƙara da cewa lokacin da ya je Ƙaramar Hukumar Gubio ya tarar cewa babu naira N100,000 a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya na tsofaffi ko sababbin kuɗin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...