Ba mu Kara Kudin Man Fetur a Nigeria ba – NNPC

Date:

Shugaban kamfanin mai na NNPCL Malam Mele Kyari ya ce babu wanda ya kara farashin mai a Najeriya.

Shugaban ya musanta iƙirarin da wasu kungiyoyin masu dakon mai suka yi a baya na cewa an ƙara farashi.

Mele ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a yau Talata kan matsalar karancin mai da ake fama da ita a Najeriya.

Cikin matsalolin da aka ambato da ake ganin su suke kawo tarnaƙi ga man sun haɗa da bangare jigilar man da kuma bangare farashin da aka gaza samun daidaito.

Mele ya kalubalanci duka masu ruwa da tsakin da suka halarci taron da su bayyana wanda ya ce musu an kara farashin man, ko kuma su gabatar da hujjar sun saye shi a sabon farashin da suka yi ikirari.

Talla

Tun a baya dai shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen ihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa BBC Gwamnatin Najeriya ta ƙara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8 inda a halin yanzu farashin ya koma naira 185 Legas da kuma 220 a wasu sassa.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

A Najeriya dai an shafe kusan shekar a guda ana karancin man fetur da kuma rashin tabbas kan farashinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...