Mutanen K/H Karaye sun yabawa Murtala Garo bisa samar musu da rijiyoyin burtsatse

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Al’ummar garin Tudun kaya da danfarwa dake karamar hukumar karaye sun yabawa tsohon kwamishinan kananan hukumomin na jihar kano Alhaji Murtala Sule Garo bisa samar musu da rijiyoyin burtsate Masu amfani da haske rana a yankin.

Shugaban karamar hukumar ta karaye Alhaji Balarabe Isyaku Karaye ne ya bayyana hakan ne yayin da yake mika rijiyoyin da aka samar ga al’ummar yankin.
Shugaban karamar hukumar yace rijiyoyin burtsaten zasu taimaka wajen magance karacin ruwa a yankunan, sannan yace nan gaba kadan Murtala Sule Garo ya yi alkawarin samar da wasu aiyukan a garin Tudun kaya da garun maje.
Ya kuma bukaci al’ummar garuruwan da su baiwa rijiyoyin burtsatse kulawar da ta dace don su jima suna amfani da su, sanann ya bukaci su cigaba da baiwa gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje hadin kai su kuma fito su zabi jam’iyyar APC a zaben dake tafe.
Talla
A jawabinsu daban-daban dagatan garin Tudun kaya Alhaji Buhari Muhammad da Malam Sulaiman Sa’id sun bayyana farin cikinsu tare da godiyarsu ga Dan takarar mataimakin gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Alhaji Murtala Sule Garo, sun kuma bada tabbacin zasu baiwa rijiyoyin burtsatse kulawar da ta dace.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...