Daga Maryam Abubakar Tukur
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce adadin masu amfani da internet a wayoyinsu a ƙasar ya kai miliyan 154.28, ƙarin kashi 37 cikin shekara takwas.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wasu bayanai da ta wallafa a shafinta na yanar gizo

Bayanan da NCC ta fitar sun nuna cewa a watan Disamban 2015 adadin masu amfani da internet a wayoyinsu miliyan 97.03 ne, amma zuwa Disamban 2022 adadin ya kai miliyan 154.28.

Bayanan na NCC sun nuna cewa kuɗin shiga da ƙasar ke samu ta ɓangaren harkokin sadarwa ya ƙaru daga kashi 8.50 a shekarar 2015 zuwa kashi 12.85 a rubu’i na uku na shekarar 2022.
Haka kuma bayanan sun nuna cewa an samu ƙaruwar masu amfani da waya zuwa kashi 116.60 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda adadin yake a 2015.