Rashawa: ‘Yan sanda a Kano sun damƙe wanda ya yi yunƙurin kuɓutar da mai garkuwa da mutane

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Rundunar ‘Yan Sanda ta kasa reshen jihar Kano ta ce ta kama wani mai Suna Alhaji Bawa ɗan asalin Shika a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna bisa zargin bai wa ɗan sanda, SP Aliyu Mohammed, da ke Sashen Binciken Manyan Laifuffuka cin hancin naira milyan ɗaya (1,000,000:00) don ya saki wani mai garkuwa da mutane da rundunar ta kama .

Kadaura24 ta rawaito hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya sanyawa hannu kuma aka aikowa manema labarai a ranar Talata.
Talla

Sanarwar ta ce, wanda aka yi yunƙurin kuɓutar da shi ɗin mai suna Yusuf Ibrahim, ɗan asalin Garin Danjibga da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara an kama shi ne a tashar motar Rijiyar Zaki da ke Jihar Kano bisa zargin garkuwa da mutane.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Sanarwar ta ƙara da cewa, jami’an samar da zaman lafiya ƙarƙashin jagorancin CSP Usman Abdullahi DPO na yankin Rijiyar Zaki suka samu nasarar kama shi bayan an bayyana shi ta hanyar wani direban mota da suka yi garkuwa da shi a hanyar Funtua zuwa Gusau, inda suka karɓi Naira 500,000 a matsayin fansa kafin su sako shi.
Haka kuma, sanarwar ta ce a yayin da aka tsaurara bincike wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya ce yana cikin waɗanda suke garkuwa da mutane tsakanin garuruwan Sheme da Yankara da Faskari da garin Kucheri dake jihohin Katsina da Zamfara, inda ya yi iƙirarin ƙungiyarsu ta kashe mutum 10, daga ciki ya kashe biyu da hannunsa.
Kawo yanzu an miƙa batun ga kotu don zurfafa bincike.
 Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya yaba dangane da haɗin kan da al’ummar Kano ke bai wa jami’ansu a bakin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...