Daga Kamal Umar Kurna
Shugaban karamar hukumar fagge Honourable Ibrahim Abdullahi Muhd Shehi ya bayyana taimakawa marayu da tallafar yaran da iyayensu keda karamin karfi da kayan koyon karatu da koyarwa a matsayin wani ginshiki wanda zai haifar da al’amma ta gari.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Alhaji Murtala Tijjani, ya bayyana hakan ne wajen rabawa daliban makaratun firamare 300 wadanda suka fito daga karamar hukumar fagge kayan sawa na makaranta wato Uniform da litattafai da kuma rabawa marayu 70 tallafin kudi naira dubu biyar biyar ga kowannensu wanda gidauniyar daya daga cikin ‘yan kishin karamar hukumar ta fagge Abdulaziz Mohd Abdullahi wanda aka fi sani da Malam wato Me Lamma foundation ta shirya a hedkwatar hisbar karamar hukumar.

Da yake jawabi tunda farko Hakimin Fagge Tafidan Kano Alhaji Mahmud Dr Ado Bayero wanda ya samu wakilcin dagacin rijiyar lemo Alhaji Nazifi Hamidan Abdulkarim ya bayyana cewa matashi dama shi ne kan gaba a kowace nahiya musamman karatun firamare daga tushe, wanda hakan ya zama wajibi a yabawa gidauniyar ta Me lamma.

Da yake ta’aliki akan makasudin daya sanya shi assasa bada tallafin, shugaban gidauniyar ta Me Lamma Abdulaziz Mohd Abdullahi wato Malam yace taimakawa masu karamin a kowace fuska musamman ilimi da marayu zai samar da ingantacciyar al’umma.
Daga cikin makaratun da suka rabauta da tallafin akwai makarantar firamare ta Gobirawa project , da kwachirin jobe firamare, da Na tsugunne firamare da Yusif Ata firamare sai kuma kurna firamare dukkaninsu a karamar hukumar ta fagge.