Daga Aisha Aliyu Umar
Wata kungiya ta duniya da ta kware wajen tantance muhawarar siyasar ‘yan takara a cikin al’umma, Dandalin tantance muhawarar siyasa (PODAF) ta taya gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano murnar kwazon da mataimakin gwamnan jihar kuma dan takarar gwamna na jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi a zabe mai zuwa. a wajen muhawarar takarar gwamna da Sashen Hausa na BBC ta shirya a Jami’ar Bayero, dake Kano, a ranar Asabar.
A cikin wata wasika da aka aika wa gwamnan kuma mai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar na Najeriya, Mista Johnson Craig, ya bayyana cewa, “Mun gamsu matuka da yadda mataimakin ka, wanda kuma shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya gudanar da bayanai a wajen muhawarar da Sashin Hausa na BBC ta shiryawa yan takarar gwamnan Kano.”
Sanarwa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24 a ranar lahadi.

Wani bangare na Wasikar na cewa, “Kungiyarmu ta ga ya zama wajibi mu taya mai girma gwamna murna bisa kyakkyawan kwazon da mataimakinsa Gawuna ya nuna, hakan kuma ya tabbatar da cewa dan takarar APC gogagge ne, kwararre, kuma dan siyasa ne mai kaunar zaman lafiya.”

Yayin da kungiyar PODAF ta taya gwamnan murna, ta yi imanin cewa, Kano tana da Mataimakin Gwamna Dr . Gawuna mai nagarta, Kuma sun jaddada cewa, muhawarar ta bayyana yadda Mataimakin Gwamna yake mai da hankali, wajen kishin kasa da kuma azamar bunkasa kasa.
“Dr Gawuna da abokin takararsa Murtala Sule Garo, suna da tare da kwarewa da gogewa musamman a sha’anin gudanar da mulki, Saboda yadda suka faro harkar tun daga tushe, Kuma hakan zai taka rawa sosai a zabukan da ke tafe. Babu shakka a Muhawarar BBC Gawuna ya burge duk wadanda suka gani ko suka saurari muhawarar.”