Daga Zakaria Adam Jigirya
Dan takarar majalissar tarayya na kananan hukumomin Kiru/Bebeji a jam’iyyar NNPP Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD,(Jarman Bebeji) ya gwanjage wasu daga cikin mutanen yankinsa da tallafin jari na kudade.
An dai gudanar da bikin bada tallafin ne a gidansa dake garin kofa a Karamar hukumar Bebeji.
Yayin da yake jawabi a wajen taron Abdulmumini Kofa ya ce ya basu jarin ne a wani bangare na yakin da yake yi da zaman kashe wanda da kuma inganta masu Kananan sana’o’i.

” Mun jima Muna bayar da irin wannan tallafin da zaku iya tunawa ma a ranar 1 ga watan 1 na shekarar 2022 sai na muka hadu anan mukai addu’o’i sannan na baiwa wasunku jari, Kuma babu shakka haka zamu cigaba da yi har sai mun fatattaki talauci a kananan hukumomin Kiru da Bebeji.” Inji kofa
Abdulmumini Jibril kofa ya kuma bada tabbacin zai cigaba da tallafawa al’ummar yankin, musamman idan ya samu nasarar lashe zaben wannan shekara ta 2023.
wasu sun rabauta da Dubu dari biyu(#200,000), Dubu dari daya(#100,000), Dubu Hamsin(#50,000), Dubu Ashirin(#20,000), Dubu Goma(#10,000) da kuma Dubu Biyar(#5,000).

Mutanen da suka amfana da wannan jari/tallafi sun hada da wakilan akwatuna, Exco na karamar hukuma da mazabu na Jam’iyyar NNPP da PDP na Kiru/Bebeji, KOKAS na Kiru/Bebeji, Wasu kungiyoyi masu karfi na mata da matasa a Kiru/Bebeji, Dagatan Kiru/Bebeji, Limaman Juma’a Kiru/Bebeji, Malaman Kwankwasiyya Kiru/Bebeji, Dalibai, Yan Social Media, Mafarauta, Yan Achaba, Mahauta da kuma mutane masu bukata ta musamman.
Wannan taro ya sami halartar yan takarkaru na Kiru/Bebeji, manyan jagorori tare da shuwagabannin jam’iyyar NNPP/PDP na Kiru/Bebeji.