Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dr. Jamil Isyaku Gwamna, jigo a jam’iyyar PDP a jihar Gombe ya koma jam’iyyar APC tare da dubban magoya bayansa.
Gwamna ya sanar da sauya shekar ne tare da dubban magoya bayansa a ranar Juma’a a Gombe yayin da yake zantawa da manema labarai.
Yace ya fice daga PDP ne Saboda rikicin cikin gida, rashin shugabanci, rashin bin doka da oda a cikin jam’iyyar da rashin hadin kai a cikin jam’iyyar PDP.
A cewarsa, shugabancin jam’iyyar PDP a jihar ya yi wa jam’iyyar mummunar illa wanda ya haifar da bangarori daban-daban a cikin jam’iyyar.

Ya ce tafiyar siyasarsa ta dogara ne kan hadin kai, daidaito da adalci kuma “idan ba a samu wadannan a cikin jam’iyyar ba to babu dalilin da zai sa mu zauna a wannan jam’iyyar.”
Gwamna wanda kuma shi ne Sardaunan Gombe ya ce PDP ba za ta iya cin zabe a jihar Gombe ba, Saboda yadda shugabancinta yake tafiyar da al’amuran jam’iyyar cikin son rai da rashin adalci.
Cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran gwamnan Ibrahim Sani ya ce jam’iyyar APC ta fi kowace jam’iyyar siyasa tsari a jihar Gombe kuma tana gudanar da harkokinta ne cikin hadin kai ba tare da wata matsala ba.
Jamil Gwamna ya yi kira ga magoya bayan sa da su hada kai da goyon bayan jama’a a fadin jihar domin ganin jam’iyyar APC ta ci gaba da rike jihar da tazarar kuri’u fiye da yadda aka samu a 2019.