Babban bankin Nijeriya CBN ya rage adadin kuɗin da za a riƙa cire wa a banki da POS

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani sabon tsarin karbar kudi daga banki wanda ya gindaya cewar babu wani mutum da zai iya cire kudin da ya wuce naira dubu 100 daga banki a sati guda, yayin da kamfanoni kuma aka sanya musu ka’idar kada su wuce naira dubu 500 a mako.

 

Sanarwar da babban bankin kasar ya gabatar, yace babu wani mutum da zai iya karbar kudin da ya zarce sama da naira dubu 20 daga tashohin karbar kudaden da ake kira POS kowacce rana.

 

Babban bankin, ta hannu Haruna Mustafa, daraktan dake harkokin bankuna yace sakamakon kaddamar da sabbin kudaden da aka sauya fasali a ranar 23 ga watan Nuwamba da kuma shirinsa na mayar da hada hadar kudade ta bankuna da ake kira ‘cashless’, ya umurci duk bankunan kasuwancin kasar da kuma hukumomin dake hada hadar kudade da su tabbatar da amfani da sabon umurnin.

 

Sanarwar ta kuma ce daga wannan lokaci, bankuna ba zasu amince da cakin-kudin da ake baiwa mutane da ya wuce baira dubu 50 ba ga wani mutum, ko kuma naira miliyan 10 ga kamfanoni.

Talla

Babban bankin yace daga wannan lokaci, takardun kudaden naira 200 kawai za’a dinga zubawa a wuraren cire kudaden da ake kira ‘ATM’ domin baiwa jama’a damar cire naira dubu 20 kacal kowacce rana.

 

Bankin ya kuma baiwa bankunan kasuwanci umurnin karbar takardun shaidu daga jama’a masu karbar kudi da suka hada da katin shaidar zama ‘dan kasa da fasfo na tafiye tafiye da lasisin tuki da lambar shaidar da ake kira BVN da shaidar cire kudi da sanya hannun babban jami’in banki kafin fitar da kudin ko kuma rubutacciyar takardar amincewa a fidda kudin daga shugaban banki.

 

Babban bankin yace yana bukatar bankunan su dinga gabatar masa da cikakkun bayanai akan yadda mutane ke daukar kudin da suka wuce kima kowanne wata domin sanya ido akai.

 

Dama shugaban babban Bankin Godwin Emefiele yace yan najeriya zasu fuskanci matukar wahala wajen fidda kudi a banki lokacin da aka gabatar da sabon sauyin kudaden da akayi watan jiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...