Yan adaidaita sahu: Gwamnatin Kano ta magantu kan wahalar da mutan kano suka sha

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Mataimakin gwamnan jihar kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna yace nan da jimawa kadan zata zauna domin sake yin duba kan sabuwar dokar hana yan adaidaita sahu bin wasu manyan tituna a Kano .

 

Talla

Mun sami labarin halin da al’umma suka shiga sakamakon Wannan doka, yanzu haka gwamnati ta bada dama a sake duba dokar don samar da abun da bazai musgunawa al’umma ba”. 

 

Mataimakin gwaman ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar larabar nan.

 

Yace gwamnati ta tura jami’ai domin duba halin da al’umma suka shiga, Kuma ta ji koke -koken al’umma, zata ɗauki matakan saukakawa al’umma tunda dama gwamnatin ta al’umma ce .

 

” Duk abun da ya kamata a yi in Allah ya so nan da zuwa an jima kadan gwamnati ta sahale mu zauna mu duba mu gani, domin a kawo masalahar Wannan al’amarin, Kuma Ina tabbatarwa al’umma cewa bi’izinin lahi za’a yi abun da al’umma zasu ji dadin sa”. Inji Gawuna 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...