Daga Rukayya Abdullahi Maida
Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya yanke wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda ya ki bin umarnin kotu.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Olajuwon ya bayar da umarnin ne biyo bayan karar da wani tsohon jami’in ‘yan sanda, Patrick Okoli ya shigar inda ya ce ya yi ritaya daga aikin ‘yan sandan Najeriya ba bisa ka’ida ba.

A cewar sanarwar mai neman hakkin nasa (Okoli) yace an tilasta masa yin ritayar dole da a watan Yuni 1992.
A ranar 19 ga Fabrairu, 1994, wata babbar kotu a Bauchi ta kalubalanci ritayar dolen da aka yi masa, ta kuma yanke hukunci a kan wanda ya nema tare da soke takardar ritayar.
Babbar kotun ta kuma bayar da umarnin mayar da mai karar bakin aikinsa tare da biyansa duk wasu hakkokinsa.
A hukuncin da ya yanke, Olajuwon ya ce a daure IGP gidan yari kuma a tsare shi na tsawon watanni uku, har sai ya bi umarnin kotun bayan