2023: Rashin ganin nasara ne yasa yan kwankwasiyya suke kai wa yan APC hari a Kano – Muhd Garba

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu
 Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta bukaci hukumar ‘yan sandan jihar da ta gudanar da kyakyawan bincike tare da gurfanar da wasu ‘yan jam’iyyar NNPP biyu, Imam Dayyabu da Nasir Sani kan jagorantar wasu ’yan jam’iyyar wajen gudanar da aiyukan ta’addanci a jihar Kano. mutane sun lalata kadarori na yakin neman zaben APC a ranakun Asabar da Lahadi a Galadanci Quaters dake karamar hukumar Gwale a jihar.
 Jam’iyyar APC, wacce ta yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Gawuna/Garo kuma kwamishinan yada labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar, ta ce yan bangar siyasar da suka kai gari da muggan makamai, ya haifar da rudani wanda ya sa mutane da dama suka samu rauni.
 Malam Garba ya bayyana cewa, wannan mummunar dabi’a barazana ce ga zaman lafiyar da ake da shi a jihar kano .
Talla
 Kwamishinan ya ce harin ya biyo bayan zuwa daurin aure dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi a yankin tare da rakiyar magoya bayan sa.
 Ya ce abin takaici ne a ce bayan faruwar lamarin Abba K Yusuf ya rika zargin jam’iyyar APC har ma ya yi kira da a kama shugabanta, Alhaji Abdullahi Abbas.
 Kwamishinan ya kuma yi Allah-wadai da kalaman batanci da tunzuri da shugaban NNPP, Haruna Umar Doguwa ya yi wanda ka iya haddasa tashin hankali a karshen makon daya gabata.
 Kwamishinan ya bayyana cewa ficewar da jama’a ke yi daga jam’iyyar NNPP da kuma irin nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a Kano na hana jam’iyun adawa barci shi ne ke tada hankulan yan NNPP saboda sun ga baza su ci zabe ba.
 Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, domin jam’iyyar na ci gaba da jan hankalin al’ummar Kano da kuma kara tunkarar nasara a 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...