Gwamnatin tarayya ta amince da Hutun haihuwa ga maza ma’aikata

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Gwamnatin Najeriya ta amince a rinΖ™a bayar da hutun haihuwa na kwana 14 ga maza masu aikin gwamnati.

 

Shugabar ma’aikata ta gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta sanar da hakan a wata takardar sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

Talla

Sanarwar ta ce β€œgwamnati ta amince da hutun haihuwa ga ma’aikata maza waΙ—anda matansu suka haihu na tsawon kwanakin aiki 14.”

 

Sanarwar ta Ζ™ara da cewa ba za a iya Ι—aukar hutun fiye da sau Ι—aya ba a cikin shekara biyu.

 

Takardar da gwamnatin ta Saka akan wannan batu

Haka nan za a iya Ι—aukar hutun ne na haihuwa huΙ—u.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related