Daga Maryam Adamu Mustapha
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan sanda sun kama Ambasada Yusuf Imam, wanda a ka fi sani da Ogan Boye, ƙusa a jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Kano.
Wani makusancin Ogan boyen wanda ya nemi a sakeye sunansa shi ne ya bayyana mana cewa an kama Ogan Boye ne tun a daren jiya Lahadi a gidansa da ke Ƙaramar Nassarawa, inda su ka kai shi shelkwatar rundunar.

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa a ka kama Ogan Boye ba, sai dai Wani makusancin Ogan boyen ya shaida mana cewa hakan ba ya rasa nasaba da rigingimn siyasa da su ka fara kunno kai tsakanin APC da NNPP a jihar.
Sai dai kuma da wakilin Kadaura24, ya kira mai magana da yawun rundunar ƴan sandan, bai samu daga wayar ba.