Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
Hukumar kula da kafafen yada Labarai ta Kasa (NBC) ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka na rufe gidan talabijin na Najeriya NTA da Gusau da kuma gidan rediyon tarayyar Najeriya Pride FM bisa zargin su da karya dokar gwamnati da aikin jarida.
Idan za a iya tunawa, a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Dosara, ya fitar a Gusau ranar Asabar, gwamnatin ta ce sauran kafafen yada labaran da aka dakatar sun hada da Gamji TV da Gamji FM da kuma Al’umma TV wadanda ke zaman kansu.
Sanarwar ta ce kwamitin tsaro na jihar ya amince da rufe tashoshin.
An umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya kama tare da gurfanar da ma’aikatan tashoshin da lamarin ya shafa da aka kama suna karya dokar,” in ji sanarwar.

Sai dai a martanin da NBC ta fitar a wata sanarwa da babban daraktan ta, Balarabe Shehu Ilelah ya fitar kuma ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, ta bukaci hukumomin tsaro da su yi watsi da kiran da aka yi na hana ma’aikatan tashoshin da abin ya shafa gudanar da ayyukansu, domin hakan baya kan doka.
Sanarwar mai taken, ‘Rufe gidajen yada labarai da gwamnatin jihar Zamfara ta yi ba bisa ka’ida ba tare da yin la’akari da dokar NBC/DGABV/PR/10/2022 ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa ta yi matukar damuwa kan matakin da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka na cewa wai dakatar da wasu kafafen yada yada daga aiki a jihar, a ranar Asabar 15 ga watan Oktoba, 2022.
“Hukumar NBC ta sanar da gwamnatin jihar karara game da girman laifin da ta aikata kuma ta bukace ta da ta gaggauta janye wannan umarni tare da neman afuwar al’ummar jihar zamfara.
“Muna kuma kira ga Hukumomin Tsaro da su yi watsi da kiran da aka yi na hana Ma’aikatan Tashoshin da abin ya shafa gudanar da ayyukansu na wanda doka ta basu dama.
“Hukumar na son kara jaddada cewa za ta yi tir da duk wani yunkuri na karya doka da oda a ko’ina ta hanyar yin amfani da kafafen yada labarai ba bisa ka’ida ba a Najeriya, kafin, lokacin da kuma bayan zaben 2023.
Sanarwar tace duk wani mutum ko wata hukuma da hake da korafi na gaskiya akan wata kafar yada labarai ta ya sanar da hukumar NBC domin ta ɗauki matakin da ya dace, ba wai a dauki doka a hannu ba.
“Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da aka dora mata bisa yadda dokar hukumar NBC t tanada, sannan an bukaci duk masu lasisin yada shirye-shirye da su tabbatar da bin doka da oda tare da kaucewa duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga mulkin dimokradiyya da zaman lafiya a Najeriya.