Daga Aliyu Abdullahi Fagge
Gwamnatin jihar zamfara ta rufe dukkanin kafafen yada labarai mallakin gwamnatin tarayya da masu zaman kansu a jihar saboda yada labaran al’amuran da suka shafi harkokin jam’iyyar adawa ta PDP.
Majiyar Kadaura24 ta Smartmedia ta rawaito cewa bugu da kari Gwamnatin ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya kama duk ‘yan jaridun da suka halarci taron.
Kwamishinan yada labarai na jihar Malam Ibrahim Magaji Dosara ne ya sanar da hakan ta gidan rediyon karamar hukumar.
Umurnin ya shafi Radio Nigeria Pride FM, NTA Gusau, Gamji FM da dai sauransu