Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bada tabbacin Cigaba da tallafawa harkokin addinin musulunci kamar yadda ya faro tun farkon gwamnatin sa .
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokaci daya jagorancin rabon kayan mauludi ga zawiyoyi da gidajen shehunnai a jihar kano a gidan gwamnatin Kano, a wani bangare na taya al’ummar musulmi murnar zagoyowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Annabi S A W.
Ganduje wanda dan takarar mataimakin gwamnan Kano Murtala Sule Garo ya wakilta ya an raba kayan ne domin taimakawa mahalarta maulidai da abun yanka da abunci don su ji dadin gudanar da bikin maulidin na bana.
“Da ma duk shekara gwamnan Ganduje yakan gudanar da irin wannan aiki na alkhairi Kuma hakan ya tabbatar da kishinsa ga addinin musulunci da Kuma Malamai dama al’ummar jihar kano baki daya” . Inji Garo
” Mun rabawa zawiyoyi guda goma shanu da Kuma bada shinkafa manyan buhu ga wasu daga cikin shehuna da manyan Malamai da muke da su a Kano a su 100, sanann mun samar da ruwan Sha da litattafai na yabo da tarihin manzon Allah S A W duk domin aji daden gudanar da Maulidin bana”.
Yace Idan al’ummar jihar kano suka zabi yan takarar gwamnan na Jam’iyyar APC zasu dora da yin duk wasu aiyukan alkhairi da gwamnan Ganduje ya faro tun a farkon gwamnatin sa.
“Ina baku tabbacin idan dan takarar mu na gwamna da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da ni mataimakin sa Idan muka cin zaben 2023 Zamu dora da Wannan aikin da ma wasu aiyukan da gwamnan Ganduje ya faro don hidimtawa to jihar kano”. Inji Garo
A nasa jawabin amadadin wadanda suka amfana ka kayan masarufin Sheikh Tasi’u wanda shi ne shugaban kungiyar khadimul islman Political yace bayawa gwamnan bisa Wannan kulawar da yake baiwa Masoya Annabi S A W musamman a irin wannan lokaci na Maulidin ma’aiki (S A W) .
“Mun ji dadin Wannan hidima da akai mana Kuma zamu yi addu’o’in don Ganduje ya cigaba da samun nasara a gwamnatin sa, kuma dole mu yiwa Gawuna da Garo addu’o’in samun nasarar zabe ko don a cigaba da wannan abun alkhairi “. Sheikh Tasi’u
Sheikh Tasi’u ya bada tabbacin zasu cigaba da yin addu’o’i da Kuma bada goyon bayan su gwamnatin Kano don ganin APC ta yi nasara a Zabe mai zuwa don a cigaba da basu kulawa a gwamnatance.