Kisan Ummita: Quanrong zai riƙa cin abincin ƙasarsu ne ba gabza ba — Gidan yari

Date:

Daga Fa’iza Bala koki

 

Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali ta Ƙasa ta bayyana cewa Geng Quanrong, wanda ake tuhuma da kashe budurwarsa, Ummukulthum Buhari a nan Kano, zai riƙa cin irin abincin ƙasarsu ne ba wai gabza ba.

 

Kadaura24 ta rawaito cewa, a jiya Laraba ne Kotun Majistire mai lamba 30 da ke zaman ta a Titin Zungura a Kano ta aike da Quanrong zuwa gidan yari, bayan da ta tuhume shi da kisan kai.

 

Alƙalin kotun, Hanif Sanusi Yusuf ya ce laifin ya saɓa da sashi na 221 na kundin laifuka, inda ya ɗage zaman kotun zuwa 13 ga watan Oktoba, ya kuma bada umarnin da a ajiye shi a gidan gyaran hali.

Talla

Sai dai kuma da ya ke ƙarin haske a kan ko ya zaman Quanrong a gidan yarin, Kakakin Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali a Kano, DSC Musbahu Lawal Kofar Nasarawa ya shaida wa Freedom Radio cewa abincin ƴan China zai riƙa ci.

 

A cewar Kofar Nassarawa, jama’a na ta tambayar ko wanne irin abinci za a riƙa bai wa wanda ake zargin.

Talla

Ya yi bayani cewa doka ta bada damar a rika baiwa fursuna, wanda ba ɗan ƙasa ba kula wa ta musamman, wato “special treatment”, inda ya ƙara da cewa “za a riƙa bashi irin abincin ƙasarsu ne ba gabza ba.”

 

Ya ƙara da cewa doka ma ta bada damar ya sanar da ofishin jakadancin ƙasar sa ko kuma ƴan uwansa da za su iya taimaka masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...