Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa
A kokarin sa na inganta harkokin ilimi dan majalisar tarayya dake wakiltar karamar hukumar Nasarawa Hon. Nasiru Ali Ahmad ya kaddamar da ginin wasu ajujuwa guda 40 wadanda za’a ginasu a makarantun firamare da sakandire dake fadin karamar hukumar Nasarawa.
Da yake kaddamar da ginin ajujuwa guda 3 a makarantar firamare gawuna Hon. Nasiru Ali Ahmad yace za’a gina ajujuwan ne domin kara inganta harkokin ilimi a tsakanin matasan karamar hukumar Nasarawa.
” Wadannan ajujuwa da zamu gina kari ne akan guda 70 da muka Samar domin inganta ilimi, kuma ina baku tabbacin zamu cigaba da bujito da aiyukan da zasu kara habbaka ilimin ‘yayanmu, saboda yanzu duniyar ta chanza duk abun da zaka yi dole sai kana da ilimi don haka zamu yi duk mai yiwuwa wajen kara daga darajar ilimi a Narasawa” . inji Hon. Nasiru Ali Ahmad
Hon. Nasiru Ali Ahmad Wanda yane dan takarar majalisar tarayya na Nasarawa a jam’iyyar APC, yace an kaddamar da ginin ajujuwan ne a mazabar gawuna domin mazaba ce ta mataimakin gwamna kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da shugaban jam’iyyar APC na Nasarawa, yace hakan tasa cikin ajujuwa guda 40 da za’a gina aka waje guda 8 a mazabar ga Gawuna.
” ina so ku sani wannan aiki da muke yiwa ilimi a karamar hukumar mu ta Nasarawa koyi muke da babanmu gwamnan kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, saboda ya dauki ilimi da matukar muhimmanci, Wanda hakan tasa ya fito da tsarin bada ilimi kyauta kuma dole a duk fadin jihar kano, wannan tasa muma muke koyi da shi”. A cewa Dan majalisar tarayyar
Yace bazai gajiya ba wajen cigaba da kai aiyukan da zasu ciyar da karamar hukumar Nasarawa gaba kamar aiyukan cigaban ilimi, lafiya Samar da aiyukan yi ga matasa da kuma bada tallafin sana’o’i domin matasa maza da mata su dogara da kawunansu.
Bayan dai kaddamar da ginin ajujuwa guda 6 a Makarantar Gawuna Primary school, da Kuma Liman Datti Primary School inda zai gina Ajujuwa 3, Aikin kuma ginin yana cikin Ginin Ajujuwa guda 40 da zai gina a fadin Karamar Hukumar Nassarawa.
Duk a yau din Hon. Nasiru Ali Ahmad ya Kaddamar da Ginin Sabon Asibiti a Mazabar Tudun Murtala, wanda shi ma daya ne daga cikin Sabbin Asibitoci guda shida da dan majalisar Nasarawar zai Samar a karamar hukumar Nasarawa.
Taron dai ya sami halartar dan takarar majalisar jiha na Nasarawa da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Nasarawa da wakilin Dan majalisa wato Rabi’u baba nabegu da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da matasa maza da mata na karamar hukumar Nasarawa.