Daga Abubakar Sadeeq
Ɗan takarar majalisar tarayya a ƙananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam a jam’iyyar APC, Hon Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da takwaransa Engr. Rabiu Musa Kwankwaso sun haɗa kai ne domin ruguza jam’iyyar NNPP domin su marawa Atiku Abubakar da Bola Tinubu baya a kakar zaben 2023.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da wakilin jaridar Kadaura24 a ranar Larabar nan.
Yace bayyana sunayen yan takarar sanatoci da majalisar tarayya, da hukumar zaɓe ta yi a jiya talata, ya tabbatar da cewa kwankwaso da malam shekarua na shirin yin Abu daya a zaben shekara ta 2023.
“ jam’iyyar NNPP mai Mayan gwari bata da ɗan takara a sanatan Kano ta tsakiya, domin sunan Shekarau aka bayyana”. Inji kwankwaso
Ya kara da cewar “akwai tabbacin Kwankwaso Bola Ahmad Tinubu zai marawa baya, kuma duk abin nan da ya faru haɗin bakin kwankwaso da Shekarau don jam’iyyar ta ruguje, sai da suka yi shawara da Kwankwaso don jam’iyyar ta yi biyu babu”.
Musa lliyasu kwankwaso yace shekarau da kwankwaso suna sane da cewa INEC zata fitar da takarar sunan shekarau a matsayin Dan takarar sanatan kano ta tsakiya bayan ya fice daga NNPP zuwa PDP.