An Rantsar da sabbin shugabannin kungiyar mata yan jarida ta kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa  (NAWOJ), reshen jihar Kano ta kaddamar da wani sabbin shugabannin kungiyar wadanda zasu tafiyar da harkokin kungiyar, na tsawon shekaru uku masu zuwa.
  A jawabin kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ya bayyana cewa gwamnatin jihar kano za ta baiwa NAWOJ cikakken goyon baya wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
  Ya bayyana shugabanci a matsayin babban kalubale kuma ya bukace su da su yi aiki tukuru tare da cike gibin da ke tsakanin mata ‘yan jarida a Kano.
Talla
  “Gwamnatin jihar za ta taimaka tare da tallafa wa sabon shugabannin wajen gudanar da ayyukansu cikin nasara.”
  A nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa (NUJ) reshen jihar Kano, Kwamared Abbas Ibrahim ya bukaci sabbin shugabannin da su tabbatar da gaskiya da rikon amana a shugabancinsu.
  Ya bukace su da su ci gaba da rike kowa da kowa domin ci gaban jihar da kasa baki daya .
Talla
  A jawabinta na kama aiki sabuwar shugabar ta bada tabbacin zata yi duk mai yiwuwa wajen ciyar da kungiyar NAWOJ Kano .
  Ta bayyana cin zarafin ‘ya’ya a matsayin wani lamari mai daure kai a cikin al’umma wanda ya kamata a magance shi yadda ya kamata.
  “A matsayinmu na ‘yan jarida dole ne mu mu yi abo wajen kwatowa masu karamin karfi hakkokinsu musamman matan da aka ci zarafinsu”. Inji shugabar
 Kadaura24 ya ruwaito cewa sabbin jami’ai sun hada da: Hafsat Sani-Usman, daga (ARTV), Aisha Ahmed, (NAN), Elizabeth Lamido (NTA), Rukkaiya Umar Radio Kano, Shamsiyya Ibrahim (NOA), Binta Kabir Usman daga ma’aukatar yada labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...