Daga Rukayya Abdullahi Maida
Yan china mazauna jihar kano karkashin jagorancin Shugaban su Mr. Mike Zhang sun yi Allah Wadai da kisan da wani Dan China yayi wa Ummulkhairi Buhari dake unguwar jan bulo a birnin kano.
Kadaura24 ta rawaito Cikin wata Sanarwar da hadinmin wakilin yan China a jihar Kano Mr. Guang Lei Zhang ya fitar a madadin dukkanin yan china mazauna jihar kano sun ce basa goyon bayan ta’addancin da guda daga cikin su yayi na kisan Ummita har gida.
Abin da Ummita ta gaya min a kan saurayinta ɗan China da ya kashe ta — Sheikh Daurawa
Sun Kuma ce kisan ta’addancin ne wanda bai kamata a bar wanda yayi shi hakan nan ba, Inda suka yi kira ga Hukumomin tsaro da su tabbatar an hukunta wanda yayi laifin dai-dai da dokar Kasar nan.
Ganduje yace dole doka ta yi aiki akan dan Chinan da ya kashe Ummita
Sanarwa tace dukkanin yan china mazauna jihar kano sun goyon bayan a hukunta wanda yayi kisa domin ya zama izina ga duk masu hali ko tunani irin nashi, sannan suka yabawa al’ummar jihar nan bisa karrama da karbar baki da suke yi a koda yaushe.