Daga Aliyu Abdullahi Danbala Gwarzo
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kama wani fitaccen mai haɗa wani abin sha da ke taɓa ƙwaƙwalwa, wanda aka fi sani da Akurkura a Kano.
Jami’an NDLEA ɗin sun cafke Qasim Ademola, inda su ka damƙe kwalabe 26, 600 na kayan mayen da aka tanada domin rabawa a fadin jihohin Arewa.
An kama kayan ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba a kan hanyar Zaria zuwa Kano, Gadar Tamburawa.
A nan ne kuma a ka cafke mai haɗa sinadarin, mai shekaru 39 ɗan karamar hukumar Akinyele, jihar Oyo da uku daga cikin masu rarraba shi a wani samame da aka yi.
Shugaban Hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya yabawa hafsoshi da jami’an rundunar a Kano bisa yadda suke ƙwazo da jajircewa wajen gudanar da ayyukan su.
Ya kuma umarce su da sauran su a fadin kasar da su ci gaba da mai da hankali yayin da suke sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.