Daga Rahama Umar Kwaru
Rahotanni da su ke fito wa daga Masarautar Buckingham sun nuna cewa Yarima Charles ya zama Sarkin Ingila, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Da yammacin Alhamis ɗin nan ne Elizabeth ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.
Daily Nigerian tace Jaridar AFP ta rawaito cewa, rasuwar ta ke da wuya, sai a ka sanar da Charles, wanda shi ke babban ɗanta, mai shekaru 73 da haihuwa, a matsayin wanda zai gaje ta.
Sarauniya Elizabeth dai ita ce mafi daɗewa wa a kan karagar mulkin, inda ta shafe shekaru 70 ta na mulki.