Yanzu-Yanzu: Sarauniyar Ingila Elizabeth ta mutu tana da shekara 96

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Sarauniya Elizabeth ta biyu, wacce ita ce mafi daɗewa a tarihin ƙasar Burtaniya, ta mutu.

 

Elizabeth ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.

 

“Sarauniyar ta mutu cikin lumana a fadarta da yammacin yau,” in ji fadar Buckingham, a cikin wata sanarwa da yammacin yai Alhamis. “Sarki da Sarauniya Consort za su kasance a Balmoral a yammacin yau kuma za su koma London gobe.”

 

Mijin Sarauniyar, Yarima Philip, ya riga ta rasuwa, wanda ya rasu a ranar 9 ga Afrilu, 2021, yana da shekaru 99 a duniya.

 

Sarauniya Elizabeth ta bar ‘ya’yanta maza uku, Yarima Charles, Andrew da Edward; da kuma mace, Gimbiya Anne; jikoki takwas, Yarima William da Harry na Wales, Gimbiya Beatrice da Eugenie na York, da Peter da Zara Phillips, da kuma Lady Louise Windsor da James, Viscount Severn. Ta kuma rasu ta bar jikoki 12.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...