Kotun ɗaukaka kara ta Port Harcourt ta rage hukuncin ɗaurin shekaru 26 da wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Yenagoa ta jihar Bayelsa ta yanke wa Yinusa Dahiru, wanda a ka fi sani da Inusa Yellow a watan Mayun 2020.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Mai shari’a Jane Inyang ta yanke wa Dahiru hukuncin ɗaurin shekaru 26 a gidan yari, bisa laifin safarar yara da kuma lalata da wata budurwa, Ese Oruru.
Dahiru, wanda bai gamsu da hukuncin ba, sai ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara, inda ya nemi ta wanke shi.
Bayan sauraron lauyoyin Yellow, Abdul Mohammed, SAN, Yusuf Dankofa, Huwaila Mohammed, Sunusi Musa da Kayode Olaosebikan, kotun daukaka ƙara ta amince da daukaka karar ta wani ɓangare.
Kwamitin da JS Iykegh ya jagoranta, ya yi watsi da ƙarar da aka shigar kan hukuncin da aka yanke wa Dahiru kan laifukan da ake tuhumarsa da shi, sai dai ya ce kotun ƙasa ta yi kuskure da ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru bakwai, wanda ya zarta iyakar da doka ta tanada.
Yayin da ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, kotun ɗaukaka kara ta ce Dahiru zai ci gaba da hukuncin ne a lokaci guda sabanin hukuncin da kotun ta yanke a jere.
Bisa wannan umarni, Dahiru zai yi zaman gidan yari na shekaru bakwai daga ranar 25 ga watan Oktoba, 2018, inda zai shaƙi iskar ƴanci watan Mayun baɗi.