Daga Maryam Abubakar Gwagwarwa
Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya sha alwashin da iznin Allah, zai kawo wa Atiku Abubakar kuri’un jihar Kano a zaben 2023 .
Yace yana da mutunensa wanda sune suka zabe shi a shekara ta 2003 lokacin da ya kayar da Kwankwaso, Kuma su suka zabe shi a 2007, don haka ya bayar da tabbacin mutanen suna nan kuma su zasu zabi Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2023.
Kadaura24 ta rawaito Malam Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na AIT kan zaben shekara ta 2023 da Kuma komawararsa jam’iyyar PDP.
” A shekarar 2003 na kayar da Kwankwaso da Ganduje a takarar kujeran Gwamna kano lokacin a Jam’iyyar ANPP, na basu ratar sama da kuri’a dubu dari shida (600,000 ), sannan a zaben 2007 sun sake tsayawa takaran Gwamna na kayar dasu, don haka a zaben 2023 zan kawo wa Atiku kuri’ar jihar Kano Insha Allah”. Inji Shekarau
Shekarau wanda ya shiga jam’iyyar PDP kwanakin baya, ya kuma kara da cewa zai hado kan mutanen sa na jihohi daban-daban dake Kasar nan, wadanda suka zabe shi lokacin da ya yi takarar shugaban kasa domin su zabi Atiku Abubakar ko a wacce jam’iyya suke a zabe mai zuwa.