Zamu daga darajar Noma don inganta Rayuwar al’ummar jihar kano – sabon kwamishinan Noma

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Sabon kwamishinan ma’aikatar Aiyukan Noma ta jihar kano Dr. Yusuf Jibril JY yasa alwashin Kara habbaka harkokin noma a jihar kano domin cigaban jihar.
Dr. Yusuf Jibril ya bayyana hakan ne lokacin da ya shiga ofishinsa a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar domn fara aiki gadan-gadan a ranar Litinin.
Yace zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya tattauna da Masu ruwa da tsaki a harkokin domin fito da sabbin dabarun yadda za’a tallafawa kanana da matsakaitan manoma a fadin kananan Hukumomin 44 da ake da su a jihar kano.
Talla
” Allah ya bamu wannan damar ce domin mu taimaki al’umma , kuma zamu tsaya tsayin daka don tabbatar da duk tallafin da ake baiwa Kananan manoma ana zuwa gare su don samar da wadataccen Abinci ga al’umma”. Inji Sabon kwamishinan
Dr. Yusuf Jibril JY wanda Kwararren lititane Kuma Dan kasuwa yace ya zama wajibi ya yi aiki tukuru don ciyar da ma’aikatar gaba da fannoni daban-daban, saboda gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya basu Amana Kuma baza su yi wasa da ita ba, har sai sun bar abun da suma za’a rika tunawa da su koda basa kan kujerar ko Kuma basa raye.
Talla
“Ina kira ga ma’aikatan Wannan ma’aikata da ku bani hadin kai don tunkarar kalubalen dake gaban mu, ko zamu magance shi don al’ummar mu su amfana su amfanar da wasu, Zamu baiwa kowa damar ya gudanar da aikin sa ba tare da katsa landan ba”. Inji Dr. Yusuf Jibril
Al’umma da dama ne daga yankin Rano Kibiya da Bunkure maza da mata, matasa da Dattawa Yan uwa da abokan arziki suka raka Dr. JY zuwa ofishinsa dake Ma’aikatar Aiyuka gona ta Jihar Kano domin fara aiki gadan-gadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Karamin Ministan gidajen da raya burane...

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...