Daga Aisha Abubakar Mai agogo
Shugaban kungiyar tsaro ta Vigilantee na jihar kano Shehu Rabi’u yace aikin kungiyar yana da muhimmanci a cikin al’umma, saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta tsaro a jihar Kano.
Yace zuwa yanzu an samu ci gaban mai tarin yawa a fadin jihar Kano ta fuskar tsaro, Kuma hakan na da alaka da irin yadda jami’an kungiyar vigilante ke gudanar da aikinsu ba dare ba rana domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shehu Rabi’u ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakiliyar kadaura24 a ofishin sa dake kano.

” Duk lokacin da kake tafiya cikin dare zaka ga jami’an suna zagayawa cikin unguwanni a tsakiyar dare, wannan ya kara taimakawa wajen inganta tsaro, Inda harkokin kwacen waya suka takaita sosai a jihar kano “. Inji Kwamandan
Yace suna daukan ma’aikata aike Wadanda shekarun su suka fara daga shekaru goma sha takwas zuwa arba’in, kuma suna yin duba na tsanaki kafin daukar ma’aikata domin kauracewa daukar bara gurbi cikin al’umma.

“Mukan dauki mata aiki na vigilante Saboda suma akwai rawar da suke takawa wajen magance aiyukan bata gari, Amma fa Muna daukar mata ne da yardar iyayen su ko mijinsu ko wani shakiki nasu, don gudun yin kitso da kwarkwata”. Inji Shehu Rabi’u
Yace akwai kyakyawar alakar aiki tsakanin su da hukumomin tsaro dake kano musamman yan sanda, Saboda su suke kaiwa masu laifi idan sun kama don yin bincike tare da tura su kotu domin girbar abun da suka shuka.