Zargin Almundahana: AA Zaura ya shigar da kara a kotun koli kan sake shari’arsa

Date:

Daga Abubakar Sadeeq
 Dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim, wanda aka fi sani da AA Zaura ya garzaya kotun koli yana neman ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, na sake sauraron shari’ar da ake yi masa bisa zarginsa da karbar dalar Amurka 1,320 daga kasar Kuwaiti.
 A ranar 13 ga watan Afrilun 2022 ne kotun daukaka kara da ke Kano karkashin mai shari’a Abdullahi Mahmoud Bayero, ta yanke hukuncin soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a ranar 9 ga watan Yuni, 2020, wanda mai shari’a Lewis Allagoa ya yanke na korar da akai dan siyasar tare da wanke shi.
 A hukuncin da aka yanke Mai shari’a Bayero ya bayar da umarnin a sake gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban wani alkali na daban banda mai shari’a Allagoa.
 “An soke hukuncin da  kotun tarayya mai lamba FHCK/CR2018/FRN ta yanke kan Abdulsalam Sale Abdulkarim wanda aka yanke ranar 9 ga watan Yuni, 2020.”
 Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a shekarar da ta gabata ta kai AA  Zaura gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kano, inda ta zarge shi da zamba a Kuwaiti ta kudin da yawansu yakai  $1,320,000 da ya samu ta hanyar zamba, Inda yace shi Kwararren magini ne da ya kware a gine-gine a Dubai. Kuwait da wasu kasashen Larabawa.
 Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta gurfanar da dan zauran a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda biyar, da ake yi masa a kan wasu manyan laifuka da suka jawo hankalin miliyoyin al’umma.
 A ranar 14 ga watan Afrilun 2022 ne Abdussalam Zaura ta hannun lauyansa, Barista Ibrahim Waru ya shigar da karar zuwa kotun koli mai kunshe da korafe-korafe guda 6, yana kalubalantar umarnin da kotun daukaka kara ta bayar na sake sauraren karar.
 Rahotanni daga Kotun Daukaka Kara, dake Kano na cewa an mika bayanan daukaka kara zuwa Kotun Koli a ranar 25 ga Afrilu, 2022.
 Jaridar kadaura24 ta kuma tattaro cewa an riga an shigar da karar a ranar 20 ga Yuli, 2022, kuma an mika wa hukumar ta EFCC.
 Kotun Koli tana nazarin sanya ranar da za ta ci gaba da sauraren karar yayin da shari’ar da ake nema ta faɗo a ƙarƙashin “tsarin ci gaba na Kotun koli.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...