Sojoji Sun Kashe yan Boko Haram 49 a Borno

Date:

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe mayakan Boko Haram 49 a wasu hare-hare ta sama da jiragen yaki na Super Tukano suka kai kan ‘yan ta’addar a jihar Borno.

 

An ruwaito cewa rundunar Operation Hadin Kai ne suka kai hare-haren ta sama a ranakun 30 da kuma 31 ga watan Agusta a sansanoninsu a Gargash da Minna da Gazuwa da ke cikin karamar hukumar Bama na jihar ta Borno.

Hukumar Karota ta Kama Wata Mota Makare da Giya

 

A cewar wani masani kan tsaro da dakile hare-haren ta’addanci, Zagazola Makama a tafkin Chadi, ya ce hare-haren ta sama na ranar 30 ga watan Agusta, sun kuma fada kan wata babbar motar ‘yan tada kayar bayan da ke tafiya tare da kashe daukacin wadanda ke cikin motar.

Inganta Ilimi: Kawu Sumaila ya Baiwa Wata Yarinya Gurbin Karatu a Jami’arsa ya Al-Istigama

A ranar 31 ga watan Agusta, an samu bayanan sirri da suka nuna mayakan na hada-hadar aikin kudi, inda nan take aka kai musu hari da kashe wasu daga ciki.

 

Shaidu sun ce an akshe akalla ‘yan ta’adda 29 a Gazuwa da kashe wasu da ke tafiya cikin mota guda hudu a Gargash, yayin da mayaka 16 kuma suka gamu da ajalinsu a garin Minna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...