Daga Ibrahim Sani Gama
Shugabancin kungiyar kasuwar abinci ta dawanau, ya sha alwashin bijiro da managartan ayyuka da wayar da kan kananan da mayan yan kasuwa domin sanin kasuwanci a zamanance don bunkasa harkokin kasuwanci da ci gaban tattaliñ arzikin jihar kano da ma kasa baki daya
Sakataren kungiyar kasuwar kwamaret Rabiu Abubakar tmTumfafi ne, ya bayyana haka a zantawarsa da wakilin kadaura24 a ofishinsa dake kasuwar anan kan
Yace kungiyar kasuwar da hadin gwiwar hukumomin kula da fitar da kayayyaki da shigowa da su, suna ta tattaunwa don ganin an bijiro da hanyoyin da za su baiwa yan kasuwa damar fitar kayayyaki da ake samarwa na cikin gida zuwa kasashen ketare, ta yadda za su inganta kasuwancinsu cikin sauki tare da samun riba mai amfanu. Yace wannan wata hanyace da zata kara kawowa Najeriya ci gaba ta fannin kasuwanci
kwamaret Rabiu ya bukaci hadin kan yan kungiyar kasuwar wajen aiwatar da shirin,wanda yace bayan wannan akwai tsare_tsare na ci gaba da kungiyar kasuwar take kokarin bijiro da su, kuma za su taimakawa al’umma da dama ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa da sauran al’ummar jihar kano ta fannoni da yawa da kuma yadda gwamnati za ta samu kudaden shiga domin bunkasa harkokin tattalin arziki.
Haka zalika, kwamaret Rabiu Abubakar Tumfafi, ya shawarci yan kungiyar kasuwar da su ci gaba da gudanar da addu’o’in da za su taimaka wajen ganin kasuwar da alamuranta sun kara habaka yadda yakamata, ta yadda za ta yi gogayya da sauran manyan kasuwannin kasashen duniya
Ya godewa gwamnatin tarayya da jiha, bisa yadda suke tallafawa harkokin kasuwanci da fannin noma,musamman wannan lokaci na damina da ya shigo.