Daga Maryam adamu Mustapha
Gwamnatin jihar kano ta bukaci da a baiwa mata fifiko da kuma basu mukamai a fannoni daban-daban don suma su bayar da tasu gudun mawar domin cigaban Al’umma jihar kano da kasa baki daya .
Mai dakin Gwamnan jihar kano farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje ce ta bayyana hakan yayin da ta jagoranci bada tallafi da mai taimakawa Gwamnan na musamman a kan harkokin cikin gida Ahmad Abbas Ladan da kuma mai taimakawa Gwamnan akan harkokin mata Hajiya zainab yayannan suka gudanar a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Mai dakin Gwamnan tace duba da yadda mata suke taka muhimmiyar rawa a kowanne bangare na rayuwar al’umma, adon haka gwamnatin jihar kano ta tsaya kai da fata dan ganin suma mata sun sami mukamai da kuma ayyukan yi a gurare daban-daban.
Ta yabawa masu taimakawa Gwamnan bisa wannan abun Alkhairi da suka yi,duba da yadda suka baiwa mata fifiko a tallafin,inda tace abun da suka yi koyi ne da gwamnatin jihar kano wajen cigaban mata a jihar .
Anasu jawabin mai taimakawa Gwamnan na musamman akan harkokin acikin gida Ahmad Abbas Ladan yace sun bada tallafin ne ga mata da matasa kimanin Dari shida da saba’in da hudu don inganta rayuwar su.
Wakiliyarmu ta Ofishin Mai dakin Gwamnan Maryam adamu Mustapha yace kayan da suka bayar sun hadar da shinkafa, kekunan dinki, rigunan Bal, buhunan taki ga manoma Dan inganta harkar noma duk a yankin Karamar Hukumar Dawakin Tofa.