Daga Safiyya Adam Haske
Shahararran jarumin masana’antar Kanywood Mustapha Badamasi Naburaska ya biya tara ga akalla Mutane 33 Waɗanda suka daure a gidan gyaran hali na gwauron dutse dake nan kano.
Jarumin wanda kuma mataimakinw na musamman ga gwamnan Kano ya biya tarar Maza 31 da Mata 2 Waɗanda suka shaki iskar yanci Sakamakon kyautayin da Naburaska ya nuna musu.
Mustapha Naburaska yace ya gudanar da Wannan abun alkhairi ne sakamakon karatowar watan Azumin Ramadana, da kuma Neman yardar Allah da Neman lada a gare shi.
” Zaman gidan gyaran hali a irin wannan lokaci akwai matsi sosai ga dan adam, hakan tasa na biya tarar su don su fito su inganta Rayuwar su na nan gaba.” Inji Naburaska
Jarumin ya bukaci mawadata dake cikin al’ummar da su Gudanar da irin wannan aikin na fitar da al’umma Daga kangin rayuwa don su nemi lada a wajen Ubangiji Kuma su kyautata Rayuwar wasu.
Anasu bangaren wadanda suka shaki iskar yancin sun mika Sakon Godiyar su ga NaBraska da kuma Mutanen da suke irin wannan fitar da mutanen daga gidan gyaran halin.
A karshe dai mutanen sun lashi matakin za suy gyara halayen su bayan sun komawarsu Cikin ga iyalan su.