Bana Cikin Waɗanda Hukumar DSS ta gayyata a Kano – Alhassan Ado Doguwa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban masu rinjaye na Majalisar wakilai ta kasar nan, Kuma Dan Majalisa dake wakilar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada Hon. Alhassan Ado Doguwa ya musanta Rahotannin da suka bayyana Cewa yana daga Cikin kusoshin Gwamnatin Jihar Kano da Hukumar ta gayyata a jihar laraba.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman gare shi Auwal Ali Sufi ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

Sanarwar tace Shugaban masu rinjaye wanda shi ne Sardaunan Rano bama ya Ƙasar nan lokacin da abun ya faru Kuma babu wata takardar gayyata da aka turawa Masa daga Ofishin Hukumar ta DSS.

“Labarin da aka yada na Cewa Ina Cikin Waɗanda aka gayyata a Hukumar DSS ba Gaskiya bane bani da masaniya akan abun da aka gayyaci Wasu akan sa ballantana ace an gayyaceni ,Ina tabbatar muku cewa ni ba Wanda ya gayyace ni”.inji Alhassan Ado

Sanarwar ta Kuma bukaci masoya da magoya bayan Alhassan Ado Doguwa da su kwantar da hankulansu su cigaba da gudanar da al’amuran su cikin kwanciyar hankali da lumana, Kuma yace Yana godiya da kaunar da suke nuna masa a koda yaushe Musamman ma al’ummar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada.

Idan za’a iya tunawa a Jiya an gayyaci wasu makusanta gwamnatin jihar kano domin su amsa tambayoyi a Hukumar DSS bisa zargin su da hannu wajen ingiza Yan bangar Siyasa yayin wasu taruka da jam’iyyar APC ta gudanar a Nan kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...